16 Oktoba 2019 - 04:35
​Dakarun Juyin Musulunci A Iran Sun Bada Sanarwan Kama Ruhullah Zam

Majiyar dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran ta bada sanarwan kama wani ba’irane makiyin JMI a ranar litinin da ta gabata.

(ABNA24.com) Majiyar dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran ta bada sanarwan kama wani ba’irane makiyin JMI a ranar litinin da ta gabata.

Tashar talabijin ta Presstv ta nakalto majiyar dakarun tana cewa Ruhullah Zam ya bude wani shafin yanar gizo mai suna Amaad News a kasar Faransa inda yake yada labaran karaya dangane da JMI da kuma kokarin cusa kiyayya tsakanin mutanen Iran.

Majiyar ta kara da cewa dakarun sun sami nasarar kama Ruhullah Zam ne ta wasu dabarbarun zamani wadanda suka shafi kafafen leken asiri a wajen kasar.

Gwamnatin kasar Faransa ce take goyon bayan Ruhullah Zam a kokarin da ya yi na hargiza al-amura a cikin JMI ta hanyar yada labaran kariya a kafafen sadarwa na zamani daga kasashen waje.

Wasu labaran sun bayyana cewa Ruhullah Zam yana da wadanda suke amfani da shafinsa na Telegram kimani miliyon 1,400,000. Kuma sau da dama ya taimaka wajen haddasa tashe-tashen hankula a cikin kasar ta hanyar yada labaran kariya.

A halin yanzu dai Ruhullah Zam ya fara amsa tambayoyi a hannun dakarun na kare juyin musulunci kafin a gurfanar das hi a gaban kotu.



/129